Читать бесплатно книгу «Wani Neman Jarumai » Моргана Райс полностью онлайн — MyBook
image
cover





















Thor yaki ya saurara ya daidaita numfashinsa a yayin da yake gangarawa tudun a gunje, ta sakiyan bishiyoyi, rasan suna ta kwarzanan sa amma bai damu ba. Ya kai wani shararriyar fili sai yaga kauyensa: gari mai kaman yana barci a shake da gidaje masu bene daya, fararen gidajen laka masu jinkar ciyawa. Iyalen da suke cikin ta basu fi dozin kadan ba. Hayaki na tashi daga dakunan dafuwa dayake yawanci an tashi ana shirya kalacen safe. Guri ne gwanin ban sha’awa, da nisa daidai – tafiyan wuni a kan doki – daga padar sarki ga mai rabewa a kan hanyan wucewa. Wani kauyen manoma ne kawai a bakin zoben, wani karamin kusa a babban tayan masarautar yammaci.

Thor ya karasa shauran karshen hanyan a guje, ya shiga sakiyar kauyen, yana tada kura a yayin tafiyan. Kaji da karnuka sai kauce masa a kan hanya suke yi a guje, sai wata tsohuwa, a tsugune a kofar gidanta a gaban tukunya dauka da ruwanda yake taffasa, tayi masa tsaaki.

“Jeka a hankali mana Yaro!” Ta fada da karfi a yayin daya wuce a guje, ya sa mata kura a wutan cikin murhunta.

Amma kuma Thor ya wuci jin kira – ba ma ita ba, ba ma kowa ba. Ya sha kwana zuwa wata anguwar gefe, saikuma wata, yana murduwa yana juyuwa cikin hanyoyin da ya riga ya lakanta a zuciya, har ya kai gida.

Gidan karami ne, mazauni mara wani muhimmancin tsari Kaman shauran, da fararen bangon laka da jinkan zana daya hadu da bangon. Kaman yawanci, daki daya da gidan ya kunsa a rabe yake, mahaifinsa na kwana a bangare daya, yan’uwansa kuma a daya bangaren; inda gidan ya sha bambam da yawanci shine, yana da ‘yar karamar dakin dafuwa a baya, anan ne kuma a ka ware Thor ya dinga kwana. Da farko, yakan cunkusu da yan’uwansa; amma a cikin lokaci sun kara girma da rashin imani da kuma waraiyya, kuma sun mayarda rashin bashi wuri abin alfa’ari. Thor yakan ji haushi, amma yanzu yana more sararin kansa, yafi son ya nisance su. Wannan ya tabattar masa da abinda dama ya sani na cewa shine wararren gidan.

Thor ya nufi kofar shiga gidansu sai ya ruga ciki ba tsayawa.

“Baba!” ya tsala da ihu, yana numfashi da kyar. “Yan silver! Suna zuwa!”

Mahaifinsa da dukan yan’uwansa uku suna zaune a sunkuye akan shimfidar cin kalacen safe, sun riga suna sanye da kayayyakin su mafi kyawu. Da jin kalmominsa sun daka tsalle suka wuce shi zuwa waje a guje, sunata buge masa kafada a yayin wucewa aguje daga cikin dakin zuwa kan hanya.

Thor ma ya bisu waje, sai duk suka fara kallon alqibla suna saye.

“Bana ganin kowa,” Drake, babbansu, yace cikin murya mai zurfi. Da mafi fadin kafadu, gashi a yanke Kaman na yan’uwansa, idanu masu launin kasa, da siraren mara soyuwar labba, ya harari Thor Kaman yadda a ka saba.

“Haka nan nima,” inji Dross, mabiyin Drake da shekara daya kawai, mai kuma bin bayansa kullun.

“Suna zuwa!” Thor ya mayar masu. “Na rantse!”

Mahaifinsa ya juyo zuwa gareshi ya kuma riko kafadunsa da rashin tausayi.

“Kuma da yaya ka sani?” ya nemi yaji.

“Na gansu.”

“Tayaya? Daga ina?”

Thor ya dan saurara; mahaifinsa ya gano shi. Dama ya san wuri daya kawai da Thor zai iya hango su dagashi kuma shine dan kololon tudun nan. Yanzu kuma Thor ya rasa yaya shi zai mayar.

“Na…hau dan tudun –”

“Da garken tumakin? Ka san bai kamata su yi wannan nisan kiwon ba.”

“Amma yau ya kasance dabam. Ya zama mun dole na na gani.”

Mahaifinsa ya kale shi a kasa, kallon kiyyayya.

“Maza ka shiga ka dibo takwuban yan’uwanka ka haskaka zabiran su, domin su zama mafi kyawun kallo kafin mutanen sarkin su iso.”

Mahaifinsa, bayan yagama magana dashi, ya juya zuwa ga yan’uwansa, wayanda duk suke tsaye a hanya suna kallon hanya.

“Kana ganin zasu zabe mu?” inji Durs, Dan autan cikin su ukun, amma yayan Thor da shekaru uku masu kyawu.

“Zasu zama wawaye idon suka ki,” mahaifinsa yace. “Suna da karancin mayaka a wannan shekaran. Yakasance musu siririyar girbi – da basu damu da zuwa ba. Kudai ku tsaya a mike, dukkanku uku, ku daga haban ku sama ku kuma tura kirjin ku gaba. Kada ku kalli idanunsu kai tsaye, amma kar ku kuma kau da idanunku gaba daya. Kuyi karfin hali da yarda da kai. Kada ku nuna gazawa. Idon kuna son ku kasance a cikin rundunar sarki, dole kuyi kamman kun riga kun shige ta.

“Ai, Baba,” yaran sa maza uku suka ansa a lokaci daya, tare da fadawa muhalli.

Yajuyo ya harari Thor daga baya.

“Me kake yi a nan har yanzu?” ya tambaya. “Ka shiga daga ciki!”

Thor ya tsaya a wurin, yana zuciya bibiyu. Baya son yaki bin umurnin mahaifinsa, amma dole ne ya tattauna dashi. Zuciyarsa na ta daka a yayin da yake musabaka. Ya nadi ra’ayin bin umurnin zai fi alheri, ya kawo takwuban, sanan ya fuskanci mahaifinsa. Kin bin umurnin gaba gadi ba zai taimaka ba.

Thor ya ruga cikin gidan a guje, ya fita ta baya zuwa runfar makamai. Ya samu takwuban yan’uwansa uku, dukkansu abubuwa na gwanin sha’awa, da rawanin wurin rikewa na azurfa mafi kyawu, muhimman kyauta da mahaifinsa yayi bautan shekaru kafin suka samu. Ya daffo duka uku, yana mamakin nauyinsu Kaman yadda ya saba, sai ya koma ya ruga a guje ta cikin gidan dasu.

Ya gagauta zuwa ga yayunsa, ya mika wa kowa takwabi daya, sanan ya juya zuwa ga mahaifinsa.

“Mene, babu man share su ne?” Drake ya tambaya.

Mahaifinsa ya juyo zuwa gareshi da rashin yadda, amma kafin yace komai, Thor ya daga murya yayi magana.

“Baba, yi hakuri. Innason nayi Magana da kai!”

“Nace maka ka share---”

“Dan allah, Baba!”

Mahaifinsa ya gwaye idanu yana kallonsa, yana kokwanto. Watakila ya gano ba wasa Thor yakeyi ba, saboda daga karshe, sai yace, “To?”

“Innason nima a gwada ni. Da sauran. Ma rundunan mayaka.”

Sai dariyan yan’uwansa ya taso kawai daga bayansa, shikuma idanuwansa sukayi jajazur mai kuna.

Amma mahaifinsa baiyi dariya bashi; ammaimakon haka, dada zurfafa kallon raininsa yayi.

“Kanason haka?” Sai ya tambaya.

Thor ya girgiza kai da nufin cewa ai.

“Shekaruna goma sha hudu ne. Na cancanta.”

“Mafi karancin shekarun da ake bukata sha hudu ne,” Drake yace da bakance, ta samar kafadansa. “Idon suka dauke ka, zaka zama mafi karancin shekaru. Kana ganin zasu zabi kamanka amadadin mutum kaman ni, da na girme maka da shekaru biyar?”

“Baka da hankali,” Durs yace. “Kuma tunda haka kake.”

Thor ya juyo zuwa garesu. “Ba daku nake Magana ba,” yace.

Ya sake juyowa ga mahaifinsa, wanda har yanzu fuskarsa take daure.

“Baba, dan Allah,” yace. “Abani wannan zarafin kawai. Abinda nake roko kenan kawai. Nasan ni karamin yaro ne, amma zan nuna kaina, a cikin lokaci.”

Sai mahaifinsa ya girgiza kansa.

“Yaro kai ba mayaki bane, ba kaman yan’uwanka kake ba. Kai makiyayi ne. rayuwanka a nan yafi dacewa. Da ni. Za ka sauke hakokin da suka rataya a wuyanka ka kuma sauke su da kyawu. Baikamata mutum yadinga manyan mafarku ba. Ka rungumi kaddara, ka koyi soyayya wa kaddaran.”

Thor ya ji zuciyarsa na tashi yayin da yake kallon rayuwansa na neman ya zube a gaban idannunsa.

Babu, yayi tunani. Haka ba zai taba kasancewa ba.

“Amma Baba---”

“Yimun shuru!” mahaifin ya furta, har muryarsa tabi iska. “Ya ishe ka haka. Gasunan zuwa. Ka bada hanya, kuma ka tabbata ka maida hankalinka a yayin da suke nan.”

Mahaifinsa ya maso ya ture Thor zuwa gefe da hanu daya, Kaman wani abu mara rai da baya son yagani. Cikaken tafin hannunsa ya mari kirjin Thor.

Wani babban kara ya taso, mutanen gari sai kwararo wa sukeyi daga gidajensu, suna ta jeruwa akan hanyoyin garin. Guguwar kura mai tasowa ya gabaci rundunan, bayan dan lokaci kadan su ma suka iso, rabin dozin din amalankun dawakai, suna manyan kara Kaman tsawa daga sama.

Sun shigo gari kaman sojojin gaggawa, suka tsaya kusa da gidan su Thor. Dawakainsu, sunata motsi a wuri daya, suna karan dawakai. Ya dauki lokaci mai tsawo kafin gajimaren kuran da suka tayar ya lafa, sai Thor yayi kokarin zalaman leka kayan kariya da sukasa da makamansu. Bai taba zuwa kusa da yan Silver kamar hakaba, sai haka yasa zuciyarsa nata bugawa.

Mayakin da yake kan magabacin dokin ya sauko. Gashinan, a zahiri, dan rundunan Silver, yana rufe da kayan kariya mai kyalli, wata doguwar takwafi na rataye a kugunsa. Yayi kama da kwatankwacin dan shekaru talatin da motsi, gwarzon namiji, tsiron gasu a fuskansa, tabo a kumatunsa, da kaucecen hanci daga yaki. Ya kasance namiji mafi muhimmacin da Thor ya taba gani, fadinsa daidai na biyun shauran, the yanayin daya nuna cewa shine mai bada ummurni.

Mayakin ya diro kan hanyan kuran, dunduniyansa suna kara a yayinda ya nufi jerin yara mazan.

Sama da kasan kauyen matasa maza da yawa sun tsaya a mike, sunasa sammani. Shiga Silver yakasance rayuwar alfahari, rayuwar yaki, rayuwar a san mutum, rayuwar kasancewa a sama – tare kuma da fili, sarauta, da arziki. Yana nufin mafi kyawun Amarya, zababiyar fili, rayuwar kasancewa a sama. Yana nufin daukaka wa danginka, kuma shiga rundunan shine matakin farko.

Thor ya karanci manyan amalankun dawakain, ya kuma fahimci cewa baza su dauki sabobbin dauka da yawa ba. Babban masarauta ne, kuma zasu ziyarci garuruwa da yawa. Ya hadiye yawu, yana mai gane cewa yiyuwan samun shigansa dan kadan ne ba Kaman yanda shi ya dauka da ba. Sai shi ya doke duka shauran yara maza – mafi yawansu kuwa gugaggun mafadata – tare da yan’uwansa uku. Wannan tasa jikinsa ya mutu.

Da mayakin ya fara takawa da dadaya a cikin yanayin shuru sai numfashin Thor na neman ya dauke, ya fara daga karshen angwa, yana zagawa a hankali. Thor ya san duka shauran yara mazan, sani na musamman. Ya san wadansunsu aboye basua son a daukesu, dukda cewa iyalensu nason su rabu dasu. Suna soron; bazasu kasance mayaka masu kuzari ba.

Thor nata fama da rashin ji da kai. Yanajin cewa shi ya cancanci a zabe shi Kaman kowane a cikinsu. Kasancewa yan’uwansa sun fishi shekaru da girman jiki da karfi baya nufin ya rasa damarsa na ya tsaya a kuma zabe shi. Yana ta jin kiyyaya wa mahaifinsa, ya kuma kusan fita daga haiyacinsa a yayinda mayakin ya kusanto.

Mayakin ya tsaya, a karo na farko, a gaban yan’uwansa. Ya kallesu sama da kasa, yayi Kaman sun yakeshi. Ya mika hanu, ya kamo daya daga cikin zabirunsu, ya fincikoshi, Kaman yana son ya gwada karfinsa.

Sai yayi murmushi.

“Baka taba amfani da takwafin ka a yaki ba, ko ka taba?” ya tambayi Drake.

Thor yaga Drake yana bari a karo na farko a rayuwansa. Drake ya hadiye yawu.

“Babu, maigidana. Amma nayi amfani dashi sau dayawa a cikin muraja’a, kuma ina fatan na—“

“A muraja’a!”

Mayakin ya fashe da dariya sai ya juya zuwaga shauran mayakan, wayanda suma suka shiga, dariya a gaban Drake.

Drake ya zama jazur da kunya. Wannan ya kasance karo na farko da Thor zai fara ganin Drake ya ji kunya. – abinda aka saba gani, shi yake kunyata wadansu.

“To dai zan tabattar na gaya wa makiyanmu su ji tsoronka – kai mai amfani da takwfinka a muraja’a!”

Taron mayakan sun sake fashewa da dariya.

Sai mayakin ya juyo zuwaga shauran yan’uwan Thor.

“Yara maza uku daga tushi daya,” injishi, yana shafan tushin gemanyan kan habansa. “Da zasu iya amfani. Dukanku agine da girma mai kyau. Duk da ba a gwadaku ba. Zaku bukaci koyaswa sosai idon har zaku samu cancanta.”

Sai ya dan saurara.

“Ina gani zamu iya neman gurbi.”

Yayi nuni dakai zuwaga bayan amalanken.

“Ku hau, kuma kuyi da sauri. Kafin na canja ra’ayi na.”

Duka yan’uwan Thor uku sun ruga zuwa amalanken, suna murmushi. Thor ya gano mahaifinsa, shima yana murmushi.

Amma bai ji dadi ba ayayin da yake kallon tafiyansu.

Mayakin ya juya ya kama tafiya gida na gaba. A nan Thor ya gagara kara hakuri.

“Yallabai!” Thor yayi kira da karfi.

Mahaifinsa ya juyo sai ya ware masa idanu, amma Thor ya wuce matsayin ya damu.

Mayakin ya saya, bayansa a juye zuwa gareshi, sai ya juyo a hankali.

Thor ya dauki taku biyu zuwa gaba, zuciyarsa tana bugawa, sai ya turo kirjinsa waje gwargwadon iyawansa.

“Baka duba lamarina ba, yallabai,” yace.

Mayakin, da mamaki, ya kalli Thor sama da kasa kaman abin wasa.

“Ashe ban duba ba?” ya tambaya sai ya fashe da dariya.

Yan bayansa ma sun fashe da dariya, suma. Amma Thor bai ko damu ba. Wannan ne lokacinsa. Ko yanzu ne kokuma babu har abada.

“Ina son na shiga rundunan!” Thor yace.

Mayakin ya taka zuwaga Thor.

“Yanzu kana son haka?”

Yayi kama da abin yana bashi dariya.

“Kuma ka kai shekaranka na goma sha hudu?”

“Na kai, yallabai. Sati biyu da suka gabata.”

“Sati biyu da suka gabata!”

Mayakin ya kyalkyale da dariya, hakama mutanen da suke bayansu.

“A cikin wannan yanayin, makiyan mu zasu tabattu a kan bari daga sun ganka.”

Thor yaji shi yana konuwa da rasin ji dakai. Dole yayi wani abu. Ba zai bari yakare haka ba. Mayakin ya juya don ya tafi – amma Thor ba zai iya barin hakan ya faru ba.

Thor yayi taku zuwa gaba sai yayi ihu: “Yallabai! Kana son kayi kuskure!”

Sanda kowa a taruwan jama’a ya ja numfashin tsoro, yayinda mayakin yasake sayawa ya juyo a hankali.

Yanzu sai ya matsa goshinsa a cikin fushi.

“Wawan yaro,” mahaifinsa yace, ya cafke Thor a kafada, “koma ciki!”

“Bazanje ba!” Thor yayi ihu, ya girgiza ya kubuta daga cafkewan mahaifinsa.

Mayakin yatako zuwa gaba ya nufi Thor, sai mahaifinsa yaja dabaya.

“Kasan horon da ake yiwa wanda ya zagi dan Silver?” mayakin ya tambaya da barazana.

Zuciyan Thor nata daka, amma ya san bazai ja da baya a yanzu ba.

“Dan Allah ka yafe masa, yallabai,” mahaifinsa yace. “Shi karamin yaro ne kuma----”

“Ba dakai nake Magana ba,” mayakin yace. Da wani kallon raini, ya tilasta wa mahaifin Thor ya juya ya koma.

Mayakin ya juyo zuwaga Thor.

“Bani ansa!” yace.

Thor ya hadiye yawu, ya gagara Magana. Ba haka yaga kasancewan lamarin a kwakwalwansa ba.

“Zagin dan Silver na daidai da zagin sarki da kansa ne,” Thor yace da ladabi, yana mayar da abin da ya koya daga tunani.

“Haka,” inji mayakin. “Wannan na nufin zan iya maka bulala arba’in in naga dama.”

“Bana nufin in zageka, yallabai,” Thor yace. Inason a dauke nine kawai. Kayi hakuri. Nayita mafarkin wannan duk tsawon rayuwana. Kayi hakuri. Ka barni na samu shiga.

Mayakin ya kalleshi, sai a hankali, yanayinsa ya yiwo laushi. Bayan dan lokaci mai tsawo, sai ya girgiza kai.

“Kai karami ne, yaro. Kana da zuciyan maza. Amma ba a shirye kake ba. Ka dawo ka samemu in an yayeka.”

Da waanan, sai ya juya ya ruga, bama kallon shauran yara mazan. Ya hau dokinsa a gagauce.

Thor, rai a bace, ya kalli tayarwan tawagan; Kaman yadda suka iso da sauri, suka tafi.

Abu na karshe da Thor yagani shine yan’uwansa, azaune a bayan rumfan amalanken karshe, suna kallonsa, da rashin aminci, suna masa dariya. Ana tafiya dasu a gaban idonsa, nesa daganan, zuwaga rayuwa mafi inganci.

Daga cikin zuciyarsa, Thor yaji Kaman yamutu.

Da hayaniyan da ya kewaya shi ya kare a hankali, duk mutanen kauyen su sun kokkoma gidajensu.

“Kasan irin wawancinda kanuna, wawan yaro?’ mahaifinsa ya haura, ya kuma cafke kafadunsa. “Kasan da zaka iya bata wa yan’uwanka sa’ansu da zarafinsu?”

Thor ya ture hannayen mahaifinsa daga jikinsa da haushi, sai mahaifin ya miko hanu ya mari fuskansa da bayan hanu.

Thor ya ji zafin abin ya mayar da hararo ga mahaifinsa. Wani bangarensa, a karo na farko, yaso ya rama marin da mahaifin ya masa. Amma ya kama kansa.

“Je ka dawo da garken tumakina. Yanzu! Kuma in ka dawo, karka sa ran zan ciyar da kai. Za ka rasa abincin daren yau, sai kayi tunani a kan abinda ka aikata.”

“Watakila bazan ma dawo ba gaba daya!” Thor na ihu yana juyawa don ya tafi, ya bar gida, ya nufi su tudun bayan gari.

“Thor!” mahaifinsa ya kira da karfi. Yan kalilan din kauyawan da suka rage a kan hanya sun saya suna kallo.

Thor ya fara shi ba gudu ba shi kuma ba tafiya ba, sai ya fara gudu, yanason ya nisanci wannan gurin gwargwadon abinda ya samu. Baima san shi ya fara kuka ba, hawaye sun mamaye fuskarsa, yayin da duk mafarkun da ya taba rike wa a zuciyarsa suka cikaro da mummunan mutuwa.

...
8

Бесплатно

0 
(0 оценок)

Читать книгу: «Wani Neman Jarumai »

Установите приложение, чтобы читать эту книгу бесплатно